Shahararren mai kuɗin nan na Afrika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa gidan da yake zama a birnin tarayya Abuja, ba mallakinsa bane. A yayin wata ganawa da manema labarai a Matatar Man Dangote da ke Ibeju-Lekki, jihar Legas, Dangote ya jaddada cewa sadaukarwarsa ga masana’antun Nijeriya shi ne babban dalilin da yasa baya mallakar gidaje a kasashen waje.
Ya bayyana cewa a baya yana da gida a Landan, amma ya sayar da shi a shekarar 1996 domin mai da hankali kan ayyukan masana’antu a Nijeriya.
- Wata Sabuwa: KEDCO Ta Yanke Wutar Jami’ar Dangote Da Ke Kano
- NPA Ta Kaddamar Da Kananan Jiragen Ruwa Don Saukaka Zirga-zirga A Matatar Man Dangote
Dangote ya bayyana cewa gujewa mallakar gidaje a biranen kamar Landan da New York yana taimaka masa wajen ci gaba da mayar da hankali kan ayyukan masana’antu a Najeriya.
“Na gane cewa idan ina da waɗannan gidajen, za a samu wani dalili ko wani don yin balaguro zuwa waɗannan wurare, wanda hakan zai kawo cikas a gare ni,” in ji shi.
Baya ga gidansa da ke Legas, Dangote yana da wani gida a Kano mahaifarsa.