• English
  • Business News
Monday, November 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Amurka Ba Ta Rabu Da Bukar Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

A kwanakin baya ne, wasu rahotanni ke ta wadari a kafofin sada zumunta na zamani da ma kafofin watsa labarai cewa, wai “Cutar COVID-19 ta riga ta kare a cikin Amurka”. Sai dai tun ba a je ko’ina ba, wasu masana a Amurka suka fitar da wani bayani dake nuna cewa, ba a shawo kan cutar ba tukuna a cikin kasar, kuma ganganci ne da rashin hankali a rika wasa da annobar. Abin dariya, wai yaro ya tsinci hakori.

A kwanakin nan ita ma jaridar Washington Post, da ake bugawa a kasar Amurka, ta wallafa wani sharhi, inda ta jaddada cewa, cutar COVID-19 ba ta kare ba a Amurka. A cikin bayanin, an ce cutar COVID-19 ta dade tana yaduwa, inda wasu mutane suka mutu sanadiyar kamuwa da kwayar cutar, kuma cutar tana ci gaba da sauyawa, tare da mamaye duniya.

  • Kasar Sin Ta Bankado Karin Shaidu Game Da Kutsen Yanar Gizo Da Amurka Ta Yi Mata

Wani sabon rahoton mako-mako game da cutar COVID-19 da cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Amurka ta fitar, na nuna cewa, ya zuwa yanzu, matsakaicin mutane dubu 60 ne suke kamuwa da cutar a kowace rana, yayin da matsakaicin karuwar mutanen da suka mutu sanadiyar cutar a kwana guda, sun kai 358.

Ban da wannan kuma, tun lokacin da cutar COVID-19 ta barke a cikin Amurka, mutane fiye da miliyan 95 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da cutar ta halaka mutane fiye da miliyan 1.

Ga mai hankali, ganin wadannan alkaluma da masana suka zayyana, ta yaya za a ce babu wannan annoba a cikin Amurka?

LABARAI MASU NASABA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

Ko dai lissafin Duna ne? Don haka, ya kamata mahukuntan kasar Amurka su bude kunne da idanunsa, su kuma fahimci abubuwan dake faruwa a zahiri a cikin kasar game da wannan annoba, tun kafin wankin hula ya kai su dare.

Domin ikirarin da jagororin kasar ke yi na kawo karshen wannan cuta, labarin kanzon kurege ne. Idan kuma suka ci gaba da yaudarar kansu cewa, babu cutar a cikin kasar, to, duk abin da ya biyo, su ne za su yi kuka da kansu. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Ci Gaba Da Zama Muhimmin Ginshiki Ga Ci Gaban Nahiyar 

November 9, 2025
An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025
Daga Birnin Sin

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
Next Post
Sojoji Sun Kai Farmaki Sansanin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3 A Kaduna.

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.