• Leadership Hausa
Sunday, February 5, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Daga Birnin Sin

Har Yanzu Amurka Ba Ta Rabu Da Bukar Ba

by CMG Hausa
4 months ago
in Daga Birnin Sin
0
Har Yanzu Amurka Ba Ta Rabu Da Bukar Ba

A kwanakin baya ne, wasu rahotanni ke ta wadari a kafofin sada zumunta na zamani da ma kafofin watsa labarai cewa, wai “Cutar COVID-19 ta riga ta kare a cikin Amurka”. Sai dai tun ba a je ko’ina ba, wasu masana a Amurka suka fitar da wani bayani dake nuna cewa, ba a shawo kan cutar ba tukuna a cikin kasar, kuma ganganci ne da rashin hankali a rika wasa da annobar. Abin dariya, wai yaro ya tsinci hakori.

A kwanakin nan ita ma jaridar Washington Post, da ake bugawa a kasar Amurka, ta wallafa wani sharhi, inda ta jaddada cewa, cutar COVID-19 ba ta kare ba a Amurka. A cikin bayanin, an ce cutar COVID-19 ta dade tana yaduwa, inda wasu mutane suka mutu sanadiyar kamuwa da kwayar cutar, kuma cutar tana ci gaba da sauyawa, tare da mamaye duniya.

  • Kasar Sin Ta Bankado Karin Shaidu Game Da Kutsen Yanar Gizo Da Amurka Ta Yi Mata

Wani sabon rahoton mako-mako game da cutar COVID-19 da cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Amurka ta fitar, na nuna cewa, ya zuwa yanzu, matsakaicin mutane dubu 60 ne suke kamuwa da cutar a kowace rana, yayin da matsakaicin karuwar mutanen da suka mutu sanadiyar cutar a kwana guda, sun kai 358.

Ban da wannan kuma, tun lokacin da cutar COVID-19 ta barke a cikin Amurka, mutane fiye da miliyan 95 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da cutar ta halaka mutane fiye da miliyan 1.

Ga mai hankali, ganin wadannan alkaluma da masana suka zayyana, ta yaya za a ce babu wannan annoba a cikin Amurka?

Labarai Masu Nasaba

An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha

Sin Za Ta Hada Hannu Da MDD Wajen Shawo Kan Kalubalen Duniya

Ko dai lissafin Duna ne? Don haka, ya kamata mahukuntan kasar Amurka su bude kunne da idanunsa, su kuma fahimci abubuwan dake faruwa a zahiri a cikin kasar game da wannan annoba, tun kafin wankin hula ya kai su dare.

Domin ikirarin da jagororin kasar ke yi na kawo karshen wannan cuta, labarin kanzon kurege ne. Idan kuma suka ci gaba da yaudarar kansu cewa, babu cutar a cikin kasar, to, duk abin da ya biyo, su ne za su yi kuka da kansu. (Ibrahim Yaya)

Previous Post

Yaki Da Miyagun Kwayoyi: Za A Saya Wa NDLEA Motoci Masu Sulke

Next Post

Sojoji Sun Kai Farmaki Sansanin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3 A Kaduna.

Related

An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha
Daga Birnin Sin

An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha

11 hours ago
Sin Za Ta Hada Hannu Da MDD Wajen Shawo Kan Kalubalen Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Hada Hannu Da MDD Wajen Shawo Kan Kalubalen Duniya

12 hours ago
Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta
Daga Birnin Sin

Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta

12 hours ago
Amurka Ba Ta Cancanci Sukar Kasar Sin Ba
Daga Birnin Sin

Amurka Ba Ta Cancanci Sukar Kasar Sin Ba

23 hours ago
Sin Ta Bukaci Japan Ta Cika Alkawarin Ta Tare Da Yin Abun Da Ya Dace Kan Muhimman Batutuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Bukaci Japan Ta Cika Alkawarin Ta Tare Da Yin Abun Da Ya Dace Kan Muhimman Batutuwa

1 day ago
Ya Kamata Amurka Ta Nuna Girmamawa Yayin Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Solomon
Daga Birnin Sin

Ya Kamata Amurka Ta Nuna Girmamawa Yayin Sake Bude Ofishin Jakadancinta A Solomon

1 day ago
Next Post
Sojoji Sun Kai Farmaki Sansanin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3 A Kaduna.

Sojoji Sun Kai Farmaki Sansanin ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 3 A Kaduna.

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Kama Wani Da Kokon Kan Mutum A Neja

‘Yansanda Sun Kama Wani Da Kokon Kan Mutum A Neja

February 4, 2023
Gwamnatin Katsina Za Ta Yi Bincike Kan Kisan Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Wa Mutum 41

Gwamnatin Katsina Za Ta Yi Bincike Kan Kisan Da ‘Yan Bindiga Suka Yi Wa Mutum 41

February 4, 2023
An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha

An Gabatar Da Shirin Tallata Bikin Fitilu Na Gargajiyar Sin A Afrika Ta Kudu Da Habasha

February 4, 2023
Kashu

Nijeriya Na Samun Fiye Da Dala Miliyan 250 Daga Kashun Da Ake Fitarwa Waje -Minista

February 4, 2023
Sin Za Ta Hada Hannu Da MDD Wajen Shawo Kan Kalubalen Duniya

Sin Za Ta Hada Hannu Da MDD Wajen Shawo Kan Kalubalen Duniya

February 4, 2023
‘Yan Bindiga Sun Kashe Alkali A Kotu A Jihar Imo

‘Yan Bindiga Sun Kashe Alkali A Kotu A Jihar Imo

February 4, 2023
Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta

Wang Yi: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Rika Tuntubar Juna Domin Kaucewa Rashin Fahimta

February 4, 2023
Tinubu Yana Kaunar Nijeriya, Ku Zabe Shi – Buhari Ga ‘Yan Nijeriya

Tinubu Yana Kaunar Nijeriya, Ku Zabe Shi – Buhari Ga ‘Yan Nijeriya

February 4, 2023
Rashin Adalci Tsakanin ‘Ya’ya Yana Jawo Fitintinu (Fatawa)

Rashin Adalci Tsakanin ‘Ya’ya Yana Jawo Fitintinu (Fatawa)

February 4, 2023
Ba Za A Kara Tsawaita Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Takardun Kudi Ba —Emefiele

Ba Za A Kara Tsawaita Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Takardun Kudi Ba —Emefiele

February 4, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.