Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya taba yin alkawarin ingiza majalisar dokokin kasar ta zartas da dokar daidaita batun adalci ta “George Floyd”, amma jam’iyyun kasar 2 ba su kai ga cimma matsaya daya kan batun ba, shi ya sa har yanzu George Floyd bai samu adalci ba. Ga shi kuma a kwanan baya, Tyre Nichols bakar fata mai shekaru 29, shi ma ‘yan sandan Amurka sun doke shi har ya rasu.
‘Yan sandan Amurka sun dade suna amfani da karfin tuwo, da nuna bambancin launin fata. Shafin Intanet na Mapping Police Violence da ke bibiyar ayyukan cin zarafi da ’yan sandan Amurka ke yi, ya samar da alkaluman dake nuna cewa, a shekarar 2022, mutane 1,186 sun mutu sakamakon wannan matsala, daga cikinsu kashi 26% ne masu asalin Afirka, duk da cewa yawansu a al’ummar Amurka bai wuce kashi 13% kacal ba.
A watan Nuwamba na shekarar bara, kungiya mai zaman kanta, mai taken “Hanyar Amurkawa”, ta gabatar da wani sharhi mai taken “Fahimtar tarihin ‘yan sanda, da karfin tuwo da suke amfani da shi a unguwannin bakaken fata”, wanda ya fayyace dalili mai tushe kan batun: daga rukunin masu goyon bayan tsarin bauta, zuwa kungiyar ‘yan ta’adda masu bin ra’ayin daukaka fararen fata a gaban komai, duk suna haifar da al’adun nuna karfin tuwo kan bakaken fata.
Abun bakin ciki shi ne, iyalan George Floyd da Tyre Nichols, suna ci gaba da kuka. Shin ko yaushe ne za su samu adalci da daidaito? (Mai zane da sharhi:MINA)