Shahararren dan wasan kasar Ingila Alan Shearer ya yi imanin cewa har yanzu Arsenal na iya lashe gasar Firimiya ta kasar Ingila duk da cewar akwai tazarar maki 9 tsakaninta da Liberpool wadda ke jan ragamar teburin gasar.
A ranar Lahadin da ta wuce ne Gunners din suka tashi kunnen doki 1-1 da Chelsea a Stamford Bridge, Gabriel Martinelli ne ya zura kwallo a ragar Chelsea kafin sabon dan wasan Blues din da ya zo daga Wolberhampton Wanderers a bana ya farke ma Chelsea kwallo dab da za a tashi daga wasan.
- Gwamnatin Kano Za Ta Fassara Litattafan Kimiyya Da Hausa – Mataimakin Gwamnan Kano
- Ma’aikatar Shari’a Ta Jigawa Ta Nada Alkalan Kotun Shari’a 19 Tare Da Karin Girma Ga Ma’aikata 157
Canjaras din da ta yi na nufin Arsenal na matsayi na 4 a teburin gasar Firimiya da maki 19 a wasanni 11 da aka buga, amma Shearer, wanda ya lashe gasar Premier tare da Blackburn Robers a shekarar 1995, yana da kwarin gwiwar cewa Arsenal za ta iya ci gaba da samun nasara don rage tazarar maki.
Makin da ke tsakaninsu da Liberpool ya na da yawa amma ina ganin Arsenal za ta iya taka rawar gani sosai, ‘yan wasansu sun samu rauni makwanni biyu da suka gabata, idan su ka dawo bayan hutun kasa da kasa za su iya bayar da mamaki domin za su dawo da cikakken karfinsu domin ci gaba da taka leda inji Shearer wanda ke rike da tarihin wanda ya fi zura kwallo a tarihin gasar Firimiya.
Don haka bai kamata ayi watsi da Arsenal ba tukuna, ina tsammanin ganin sakamako mai kyau daga garesu domin kuwa su na da jagoranci mai kyau,wasa na gaba da Arsenal za ta buga shi ne wanda za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a filin wasa na Emirates Stadium da ke birnin Landan.
Bayan wasan da Forest, za su je Portugal don karawa da Sporting Lisbon a gasar zakarun Turai,sannan su koma wasan Firimiya a gidan West Ham kafin su yi wasa da Manchester United.