Aiki Ya Ki Ci Ya Ki Cinye Wa
Duk da yake gwamnati ta sha daukar alkawura na kammala aikin dakin karatu na kasa, wanda ya tsaya fiye da shekara 18, yayin da kayan da aka sa wajen fara ginin suka fara lalacewa.
Dakin karatun yana a Fuloti mai namba 35, Cadastral Business District a cikin babban birnin tarayya Abuja, tun farko an ba kamfanin Reynolds Construction Company kwangilar a shekarar 2006 lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
- Zanga-zanga: Hukumar DSS Ta Kama Jagoran #EndbadGovernance A Abuja
- Ƴansanda 2 Sun Mutu, 3 Sun Jikkata Bayan Arangama Da Ƴan Shi’a A Abuja
A lokacin an ba da kwangilar a kan kudi naira bilyan 8. Da milyan dari tara, wanda aka sa ran za a kammala shi cikin shekara hudu.
Binciken da LEADERSHIP ta yi ya gano ranar Litinin ta wannan makon aka cika shekara fiye da 18 tun lokacin da aka ba da kwangilar gina dakin karatun sai dai duk da hakan babu wasu alamu da suka nuna ana samun wani ci gaba dangane da kammala ita kwangilar.Fiye da kusan shekara da bada kwangilar, har ila yau ta kasance babu wasu alamun da ke nuna ana ci gaba da aikin.
Bayan an kasa kammala aikin sai gwamnatin tarayya ta sake ba da kwangilar a watan Maris shekarar 2010 inda aka bada wata 21 na lokacin da za a kammala kwangilar, kan kudi Naira bilyan 49.6. Duk da hakan babu wani abinda ke nuna akwai wani ci gaba
Binciken da aka yi ya nuna cewa matsalar lamarin kudin kwangilar yana da nasaba ne da yadda dala take kara tin tsada, da sauran wasu abubuwa, ya sa abinda ya hadu da matsala ga gwamnatocin da suka gabata, su sake zama da ‘yan kwangila domin a kammala aikin.
Kafin ya mika wa Shugaban kasa Bola Tinubu mulki, tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da amsar aikin da kuma samar da kudadi da hukumar kula da ilimin manyan makarantu (TETFUND).
Lokacin da Ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ya fara aiki a matsayin Ministan ilimi a shekarar 2023, ya yi alkawarin zai ci gaba da kuma kammala aikin nan da shekara ta 2025.
Mamman ya ba da tabbacin cewar dan kwangilar da yake aikin zai dawo wurin, domin ya kammala aikin.
Ya ce“Wannan aikin yana da matukar amfani ga Nijeriya, ga shi kuma ba a kammala shi ba abin ya kusa shekara 20. Mun san muhimmancin dakin karatu, ba wa ma maganar dakin karatu na kasa ba. Don haka matakin da ya dace duk wanda yake da abinda zai yi dangane da wannan aiki, to ya dawo wurin aiki.
“Akwai matsaloli nan da can, amma za a kammala aikin cikin kusan wata 21. Muna yin kira da kamfanin da aka ba kwangilar, ya kammala aikin, saboda aikin ya dauki lokaci mai tsawo, don haka aiki irin wannan bai kamata ayi ta tafiyar Hawainiya ba.
“Don haka koma menene matsalar aikin, mun dauki niyyar kammala shi kamar yadda Ministan ya furta shekara daya data gabata.
Sai dai kuma wakilinmu wanda ya ziyarci wurin bada dadewa ba ya gano bai lura da wata alama ba ko alamun da za su nuna ana samun cigaba ba dangane da aikin dakin karatu, yayin da ziyarar da aka kai wurin da ake aikin ba wani abinda zai burge wanda ya je wurin.
Wannan aikin da aka fara ba a kammala ba ya jawo maganganu daban-daban daga dalibai, masu hrakar koyar da dalibai, inda suke kiran daukar mataki ba da dadewa ba, domin kammala shi saboda ya amfani al’ummar yanzu tare da wadanda za su kasance nan gaba.
A hirar da suka yi da LEADERSHIP, daliban Nijeriya a karkashin inuwar kungiyar dalibai ta kasa (NANS) da masu ruwa da tsaki daban- daban sun yi kira da a dauki matakin gaggawa domin a kammala ginin dakin karatu na kasa domin kuwa aikin ya dade ba a kammala gina shi ba.Ta nuna rashin jin dadinta akan cewar aikin ya tsaya shekaraIt 18 duk kuwa da yake gwamna tocin da suka shude sun yi alkawarin yin hakan.
Da yake furta albarkacin bakinsa jami’in hulda da jama’a na kungiyar Komrade Gundu Mimidoo Joy yace da aikin kowa yana yi ma shi Kallon wuri ne da zai amfani al’ummar Nijeriya musamman ma wadanda su masana ilimi ne, amma yanzu ya kasance wani wurin da aka yi watsi da shi ba tare dayin la’akarin ci bayan ilimi bane ba.
“Dalibai na yi ma shi aikin wani abu da yake da muhimmanci wajen cigaban lamarin koyarwa domin,a samu ilimi mai inganci.Dakatar da shi abin ya wakilci gazawar gwamnati ta ba ilimi kulawar data kamata.Shi yasa wannan tsayawar aikin ya kara bada gudunmawa ta bangaren lalacewar ko rashin ingancin yadda makarantu suke a fadin tarayyar Nijeriya.