Dan wasan tsakiya Luka Modric ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi a Real Madrid ta tsawon shekara guda, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kungiyar har nan da 2024.
Dan wasan tsakiya na Croatia wanda kwantaraginsa ya kamata ta kare a bana, an ta jin bayanan cewa yana shirin komawa gasar kwallon kafa ta Saudiyya da ake kira Saudi Arabia Pro League.
Dan wasa Modric mai shekara 37, ya buga wa Real Madrid wasanni 488, ya ci La Liga uku da Champions biyar tun bayan komawarsa kungiyar daga Tottenham a shekarar 2012.
A shekara ta 2018, Modric ya ci kyautar Ballon d’Or lokacin da kasarsa ta je wasan karshe a gasar cin Kofin Duniya sai dai bayan sanarwar da aka fitar kan sabuwar kwantaragin nasa a Madrid babban birnin Sifaniya, Modric ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ” Gida dadi Gida dadi”.
Modric ya bi sawun ‘yan wasa irinsu Toni Kroos da Dani Ceballos da kuma Nacho Fernandez wajen tsawaita kwantaraginsu a kungiyar a bana, kuma har yanzu ana musu kallan manyan ‘yan wasan kungiyar da ta lashe gasar Zakarun Turai sai 14. Tuni Real ta dauki babban dan wasan tsakaiya na Ingila, Jude Bellingham daga kungiyar Borussia Dortmund domin karawa tsakiyarta arfi da kuma gogayya tsakanin yan wasanta.