Dan gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammad Sani Abacha, Sadiq Sadiq S Abacha, ya kare mahaifinsa inda ya ce tarihi ba zai taɓa mantawa da irin kokarin da mahaifinsa ya yi ba, duk da irin sukar da ake masa bayan rasuwarsa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Sadiq Abacha, ya bayyana mahaifinsa a matsayin wanda ya bar tarihi mai kyau kuma ba za a taɓa mantawa da shi ba.
- Ramadan: Maryam Abacha Ta Nemi Attajirai Su Tallafa Wa Mabukata
- Mutane 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Neja
“Abacha har yanzu kai kake tsonewa wasu ido duk da baka raye. Tarihi ba zai taɓa mantawa da kai ba a matsayinka na shugaba na gari, duk yadda suka so su bata maka suna a matsayi na na danka ina alfahari da kai a yau. Tabbas kai ne suke fatan su yi rayuwa irin taka” in ji Sadiq Abacha.
Kalaman na Sadiq sun zo ne, kwanaki kadan bayan tsohon shugaban kasar nan na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Mai Ritaya) ya kaddamar da littafinsa wanda ya haifar da cece-kuce, musamman a inda ya tabo batun zaɓen ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 da aka soke zaben a karkashin mulkin janar Babangida, matakin da Babangidan ya ce marigayi Sani Abacha ne ya soke zaɓen ba tare da sahalewarsa ba.
A cikin littafin, Babangida ya tabbatar da cewa zaɓen wanda, Chief Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola ya lashe, an yi shi cikin adalci kuma ingantacce amma ya ce bai san dalilin da ya sa Abacha ya soke zaɓen ba.
Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin.
Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp