Majalisar Dokokin jihar Gombe har yanzu ba ta tantance zababbun kwamishinoni 17 da gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ya tura mata ba, kwanaki 38 da suka wuce.Â
A ranar 28 ga watan Yulin 2023 ne gwamna Inuwa Yahaya ya gabatar da jerin sunayen Kwamishinonin ga Majalisar Dokokin jihar, kwanaki 60 bayan rantsar da shi a matsayin gwamna karo na biyu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya mika jerin sunayen ga akawun Majalisar Dokokin jihar, Barista Rukaiyatu A. Jalo, daga baya kakakin Majalisar, Abubakar Mohammed Luggerewo ya gabatar da sunayen a gaban kwaryar Majalisar.
Shida daga cikin zababbun Kwamishinonin sun yi aiki da Inuwa a zangonsa na farko su ne Dakta Habu Dahiru (Yamaltu/Deba), Barista Zubairu Mohammed Umar (Funakaye), Dr Aishatu Umar Maigari, Muhammad Gambo Magaji (Dukku), Alhaji Nasiru Mohammed Aliyu (Yamaltu/Deba) da Sanusi Ahmed Maidala (Akko), su na cikin zababbun mambobin majalisar zartaswa ta jihar 17.
11 da suka kasance sabbi su ne; Abdulkadir Mohammed Waziri (Akko LGA); Adamu Inuwa Pantami (Gombe); Mijinyawa Ardo Tilde (Funakaye); Mohammed Shettima Gadam (Kwami); Asma’u Iganus (Shongom); Mohammed Saidu Fawu (Billiri); da Salihu Baba Alkali (Nafada).
Sauran Kwamishinonin da ke zaman jiran tantancewa da sahalewarar Majalisar su ne Dr Barnabas Malle (Kaltungo), Dr Usman Maijama’a Kallamu (Kwami), Rtd. Lt. Col. Abdullahi Bello (Balanga), da Dr Abdullahi Bappah Garkuwa (Gombe).
Jim kadan bayan gabatar da jerin sunayen, kakakin Majalisar jihar ya sanar da tafiya hutun Majalisar na mako uku da za su dawo a ranar 21 ga watan Agustan.
Amma mako biyu bayan karewar wa’adin hutun da suka ce sun tafi, ‘yar yanzu ‘yan Majalisar ba su zauna domin fara aikin tantance Kwamishinonin da gwamnan ya aika musu ba.
Wani ma’aikacin Majalisar da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa gazawa wajen tantance Kwamishinonin bai rasa nasaba da rikicin da ke tsakanin majalisar dokoki da majalisar zatarwar jihar sakamakon ‘rashin biyansu alawus-alawus’.
Ya ce ‘yan majalisar a makon da ya gabata sun hadu, da nufin shawo kan rikicin domin ganin sun tantance Kwamishinon.
Sai dai daraktan yada labarai na majalisar, Abubakar Mohammed Umar, ya ce, ‘yan majalisar za su dawo zamansu a ranar Talata.
Ya tabbatar da cewa bayan dawowar nasu za su tantance kwamishinon da gwamnan ya tura musu.