Ranar 3 ga wata, bangaren ‘yan sandan birnin Akron da ke jihar Ohio ta kasar Amurka ya wallafa bidiyon da aka dauka kan yadda ‘yan sanda suka harbi Jayland Walker, dan asalin Afirka har ya mutu a kwanan baya.
Bangaren ‘yan sandan ya yi shelar cewa, ‘yan sanda 8 sun yi harbe-harbe fiye da 90, wadanda suka jikkata sassa fiye da 60 na jikin Jayland Walker, a cewar likitan dake taimakawa ‘yan sanda.
A jajibirin ranar 4 ga watan Yuli, dake zama ranar samun ‘yancin kan Amurka, mutuwar Jayland Walker ta sanya alkawarin da aka yi cikin “sanarwar samun ‘yancin kai” ta Amurka, wato babu wanda ya fi wani, ya zama abun dariya.
Jayland Walker ya rasa ransa ne yayin binciken da aka yiwa masu tuka motoci. Bisa binciken da jami’ar Stanford ta Amurka ta yi kan binciken masu tuka motoci fiye da miliyan 100 da ‘yan sandan Amurka suka gudanar, an ce, masu tuka motoci ‘yan asalin Afirka sun fi takwarorinsu fararen fata fuskantar yiwuwar irin wannan bincike har 20%. Kana muddin ‘yan sandan sun dakatar da motocinsu, to, sun fi takwarorinsu fararen fata fuskantar yiwuwar gudanar da bincike ko’ina har sau 2.
Baya ga cin zarafin mutane yayin da ‘yan sanda suke aiwatar da doka, ana kuma nuna bambanci tsakanin kabilu a sassa daban daban na zamantakewar al’ummar Amurka bisa tsari.
A watan Yunin bana, wata kungiyar aiki ta musamman ta jihar California mai kula da tsarin bayi da illolinsa kan ‘yan asalin Afirka, ta fitar da wani rahoto mai shafuka 500, inda ta nuna cewa, ya zuwa yanzu ana nuna wa ‘yan asalin Afirka bambanci a fannonin wurin kwana, ilmi, kiwon lafiya samun aikin yi da dai sauransu.
A yayin da ake bikin ranar 4 ga watan Yuli, shin ‘yan siyasan Amurka sun iya cimma burin wadanda suka kafa Amurka yau shekaru fiye da dari 2 da suka wuce, yayin da kasarsu take fuskantar tashe-tashen hankula, raba kan al’umma da matsalar bakin ciki? (Tasallah Yuan)