Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce kashe-kashen da ke faruwa a jihar ta’addanci ne tsantsa da wasu ke aikatawa a kan jama’ar jihar, kuma dole a tunkare shi a kan ayyukan ta’addanci, idan har ana so a yi nasarar dakatar da kisan mutane da barnata dukiyoyi.
Ya bayyana haka ne a jawabinsa na sabuwar shekara.
- Goron Barka Da Shiga Sabuwar Shekarar 2024 Daga Jawabin Shugaban kasar Sin
- Shugaban CMG Ya Aike Da Sakon Barka Da Sabuwar Shekara Ga Al’ummun Ketare
Mutfwang, ya ce a tsakanin watan Afrilu da Yuni na 2023 an kashe mutane 400 yayin da ‘yan ta’addan suka kashe mutane fiye da 160 a karshen shekarar.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce kuskure ne a alakanta harin da aka kai wa mutane a matsayin rikicin manoma da makiyaya.
Ya sanar da cewa, ya ware mako guda don zaman makoki a fadin jihar, tun daga ranar Litinin zuwa ranar 8 ga watan Janairu, 2024.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar su dukufa da yin addu’oin neman Ä·ariya daga masu mugunta da suka tasar wa jama’ar jihar.
Da yake tsokaci kan lamarin, Sanata mai wakiltar tsakiyar Filato, Diket Plang ya ce babbar matsalar ita ce yadda ‘yan ta’addan ke mamaye gonaki da gidajen wadanda suka kora, suna kuma aikin hakar ma’adinai.
Sanatan ya ce kan haka ne takwaransa a Majalisar Dattawa, Simon Lalong ya bukaci a samar da hukuma da za ta inganta jihar.
Tuni dai gwamnatin tarayya ta amince da tura karin dakaru a yankunan da ke da matsalolin tsaron, don kawo karshen su.