Farfesan kwalejin nazarin harkokin doka na jami’ar Stanford John Donohue, ya taba rubuta wata makala a mujallar The Atlantic da ake wallafawa wata-wata, inda ya bayyana cewa, hare haren bindiga sun zama matsalar da Amurka ta kasa warware su.
An tabbatar da wannan ra’ayi a karshen makon jiya, lokacin da ake murnar ranar samun ‘yancin kan Amurka, A ranaikun Asabar da Lahadi da suka gabata, an samu aukuwar hare haren bindiga a wurare daban-daban a Amurka, inda a kalla mutane 60 suka mutu ko kuma jikkata. Musamman ma sakamakon harin bindiga da ya faru a safiyar ran 2 ga wata a birnin Baltimore, wasu mutane 2 sun mutu yayin da wasu 28 suka jikkata, ciki har da yara kanana 14.
Rahotanni na cewa, a bana kawai, hare haren bingida masu tsanani har sau 338 sun auku a kasar Amurka, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 397, yayin da wasu 1,414 suka jikkata.
Amurka tana daukar kanta a matsayin abin koyi wajen kare hakkin Bil Adama, amma ga abin da ya faru, ya rushe wannan suna. Kuma burin al’ummar kasar na kayyade mallakar bindiga, ya zama abin da ‘yan siyasar kasar ke amfani da shi wajen yin takara a tsakanin jam’iyyun kasar. Sakamakon matukar son cimman burin siyasa da wasu ‘yan siyasa suke yi, sam ba za a iya warware matsalar hare haren bindiga a Amurka ba. (Mai zana da rubuta: MINA)