Kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram ta kai wasu hare-hare guda biyu a ranar Lahadin da ta gabata da kuma ranar Talatar makon nan inda suka yi ta’adi a Jihar Borno.
Hari na farko da suka kai a daren Lahadi a ofishin ‘yansanda na Jakana da ke Karamar Hukumar Konduga a Jihar Borno, ya yi sanadin mutuwar wani direban ‘yansanda da wata mata.
- An Tarwatsa Masu Zanga-zanga Kan Kokarin Kunna Wuta A Kofar Gidan Gwamnatin Kano
- Zanga-zanga: Kungiya Ta Gudanar Zanga-zangar Lumana A Jihar Filato
Maharan sun kuma kona motocin sintiri guda biyu na ‘yansanda da na ‘yan sa kai (CJTF), tare da wani babur, sannan suka sace makamai da alburusai.
Jakana, tana da tazarar kilomita 45 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
A cewar majiyoyin yankin, ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, inda suka yi artabu da jami’an tsaro a wani kazamin fadan da ya dauki tsawon sa’oi kusan uku ana gwabzawa. Daga karshe ‘yan ta’addan suka ci karfin jami’an tsaron.
Shugaban karamar hukumar Konduga, Hon. Abbas Ali Abari, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin LEADERSHIP.
A hari na biyu kuma a ranar Talata, ‘yan ta’addan sun kashe wani babban akanta na sashen ilimi a Karamar Hukumar Damboa da ke Jihar Borno, Shettima Mustapha yayin da wani bom da suka dasa a kan hanya ya fashe.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, wani abokin marigayi Mustapaha da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “tabbas akantanmu mutumin kirki, Shettima Mustapha ya rasu a wani harin bom yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri daga Damboa a yau (Talata).
“Muna cike da jimamin wannan babban rashi kuma muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa da sauran ‘yan uwa. Allah ya rahamshe shi”.
Bom din ya kuma raunata wasu mutane da motarsu ta bi ta kai cikin rashin sani.
Majiya da dama sun bayyana cewa al’amarin ya auku ne da rana tsaka a ranar Talatar yayin da sojoji da sauran jami’an tsaro suke rakiyar daruruwan masu ababen hawa daga Damboa zuwa Maiduguri.
Wadannan hare-hare dai sun kara tayar da hankulan mutane tun bayan wadanda wasu ‘yan mata masu kunar bakin wake suka kai a Karamar Hukumar Gwoza da ke Jihar Borno, kimanin wata daya da ya gabata, inda suka kashe akalla mutum 42 da kuma raunata wasu 100.
Hanyar Maiduguri zuwa Damboa dai ta zama tarkon mutuwa bayan wasu munanan hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai da suka yi sanadin kashe mutane da dama kafin lokacin da sojojin suka sake bude hanyar don bai wa al’ummar Damboa da wasu sassa na Chibok damar zuwa Maiduguri ta hanyar, yayin da su kuma mutanen Biu sai sun bi ta Buni Yadi zuwa Damaturu tsawon kilomita 300 kafin su isa Maiduguri, babban birnin jihar.