Wata kungiya mai suna Initiative for Better and Brighter Nigeria (IBBN) ta bi sahun masu zanga-zangar adawa da wahalhalun da ake fama da su a fadin kasar nan.
Mambobin kungiyar da suka yi dandazo a hanyar tsohon filin jirgin sama da ke Jos, babban birnin jihar sun gudanar da zanga-zangarsu cikin lumana.
- Ku Ci Moriyar Damarmakin Da Gwamnatin Tinubu Ta Samar Maimakon Zanga-zanga – Minista
- Tinubu Masoyin Arewa Ne Ba Kamar Yadda Wasu Ke Juya Maganar Ba – Shettima
Shugaban kungiyar, Annabi Isa El-buba ya ce masu zanga-zangar za su je gidan gwamnatin Rayfield ne, inda za su mika takardar bukatarsu ga Gwamnan Jihar Filato,Kaleb Mutfwang.
Talla