Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa Nijeriya ta fi zaman lafiya a yanzu fiye da shekaru biyu da suka gabata, inda ya bayyana cewa, an samu raguwar hare-haren Boko Haram, da ‘yan bindiga da kuma tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma musamman a fadin yankin Arewa.
Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa na kwanaki biyu da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, Ribadu ya danganta nasarar ga umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na samar da tsarin tsaro na kasa baki daya.
- Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu
- Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina
Ya ce, jihar Kaduna kadai an samu rahoton kashe-kashe 1,192 tare da yin garkuwa da sama da 3,348 a gwamnatin da ta gabata.
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya.
Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina.
A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa.
Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da tsaron kasa. “Nijeriya ta fi zaman lafiya a yau fiye da shekaru biyu da suka gabata, kuma muna ganin romon sabon tsarin tsaron kasa da aka tsara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp