Tutar kungiyar al-Ka’ida na kadawa a filin jirgin sama bayan wasu ‘yanbindiga sun jefa tsimma mai ci da wuta a cikin injin jirgin sama, wasu kuma suka fantsama sashen alfarma na filin jirgin suna harbe-harbe lokacin da suka nufi wani jirgin hukumar ba da tallafi na Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS).
Hotunan da aka dinga yadawa na maharan da suka kai farmaki ranar 17 ga watan Satumba kan filin jirgin sama na Birnin Bamako da ke Mali, sun fito da matsalar tsaro fili a wurin da ya kamata a ce na cikin mafiya tsaro a yankin Afirka ta Yamma.
- Akwai Bukatar Shugabannin Arewa Su Farka – Sarkin Fawa
- Xi Ya Yi Kira Ga Ma’aikatan Masana’antu Da Su Ba Da Gudummawar Farfado Da Arewa Maso Gabashin Sin
An kuma kai wa cibiyar horarwa ta jami’an tsaron Gendarmerie hari da ke yankin Faladié. Mazauna yankin sun dauki bidiyon yadda hayaki ke tashi daidai lokacin da ake jin karar tashin bamabamai da harbe-harbe.
Wani bidiyon ‘yanbindigar da ya tayar da hankali kuma shi ne wanda aka ga mahara masu kananan shekaru na kintsa kansu kafin kai har-haren.
Sojojin da ke mulkin Mali ba su bayyana mutanen da aka kashe ba a harin, kawai dai an ce wasu jami’an tsaron sun rasa rayukansu.
Amma da alama mutanen da suka mutu za su kai 80 zuwa 100 tare da raunata wasu 200 ko fiye.
Adadin ka iya kunsa ko akasin haka na maharan, kuma tuni dakarun gwamnati suka sake kwace iko da filin jirgin da ke Senou, da kuma barikin Faladie.
Kasar ta afka rikici ne tun daga 2011, lokacin da ‘yan kabilar Abzinawa masu neman ballewa suka hada kai da masu ikirarin Jihadi kuma suka kwace iko da Binrin Timbuktu, da Gao, da sauran garuruwan da ke Arewacin kasar.
An sha kai wa Birnin Bamako hare-hare a baya. A 2015, wani hari kan otel din Radisson Blu ya yi sanadiyyar kashe mutum 20, sannan wasu biyar suka mutu a harbe-harben da aka yi a wani wurin cin abinci na unguwar Hippodrome.
A 2017, hari kan wurin yawon bude-ido da ke wajen birnin ya kashe akalla mutum hudu.
A 2020, Kanar Assimi Goita, wani kwamandan yaki, ya jagoranci juyin mulki kan zababbiyar gwamnati saboda zarginta da gazawa wajen kawo karshen matsalar tsaron.
Daga baya aka kafa gwamnatin rikon kwarya, amma a watan Mayun 2021 Kanar Goita ya sake jagorantar juyin mulkin, inda ya kafa kansa da abokan aikinsa a matsayin jagorori.
Amma duk da mayar da hankali kan taro da kuma daukar hayar dakarun haya na Rasha mai suna Wagner don taimaka wa sojojin kasar wanda ya jawo lalacewar alaka da Faransa da kuma korar dubban sojojin kasar daga Mali masu mulkin yanzu ba su fi gwamnatin da suka gada kokari ba.
An fi fafata yakin a yankunan sahara da ke Arewacin kasar, da kuma tsakiyar kasar, inda ake yawan samun rikici tsakanin manoma na kabilar Dogon da kuma makiyayan kabilar Peul (Fulani) game da kasa da kuma ruwan sha na kiwo.
Sai dai kuma a watan Yulin 2022 masu ikirarin jihadi sun kai hare-hare biyu a kusa da garin da zimmar auka wa barikin soja na Kati da ke da nisan kilomita 15 kacal daga Bamako.
Sai dai dakarun gwamnati sun yi nasarar dakile harin suna cewa ‘yanbindiga biyu kawai aka kashe a harin. An alakanta harin da kungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wacce ita ce mafi girma a kasar mai alaka da al-Ka’ida.
‘Yan makonni bayan nan kuma Faransa ta kammala kwashe sojojinta bayan gwamnatin sojin ta kore su. Daga nan kuma, sai suka nemi dakarun Majalisar Dinkin Duniya su fice daga 14,000 su fita daga kasar.
Saboda haka, ko gwamnatin Goita za ta iya hofantar da harin da aka yada wa duniya kamar yadda ta yi bayan harin Yulin 2022?
Yanayin tsaro a Afirka ta Yamma ya sha bamban da na 2022.
A yankin tsakiyar Sahel, kungiyar JNIM da sauran masu ikirarin jihadi kamar Islamic State in the Greater Sahara (ISGS), na ci gaba da nausawa Kudanci.
Gwamnatin soja ta Burkina Faso mai makobtaka da ke kawance da Mali da Nijar a kawancen Alliance of Sahelian States (AES), ita ma ta rasa iko da yankuna da dama, musamman a yankunan karkara.
A Nijar ma, ‘yanbindigar na ci gaba da kai hare-hare a Yammaci, har ma da kusa da Yamai babban birnin kasar.
Bugu da kari, yanzu maharan kan nausa zuwa Arewacin kasashen kuma kusa da Togo da Benin. A Ivory Coast, an dakile su ne sakamakon kokarin sojin kasar da kuma ayyukan raya kasa da gwamnati ke yi.
Saboda haka yanayin tsaro a yankin yanzu ya tsananta sama da kowane lokaci a baya.
Sai dai lamarin ya dan sha bamban a Mali.
A shekarar da ta gabata dakarun gwamnati suka yi nasarar kwace garuruwan Arewaci da ke hannun Abzinawa, wadanda suka saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin farar hula a 2015 amma kuma sojojin suka soke.
Duk da cewa mayakan sun bai wa dakarun Mali da abokansu na Wagner wahala a Tinzaouaten da ke cikin rairayin Sahara, har yanzu gwanatin ce ke rike da ikon biranen yankin.
Wannan kokari na kwato wurare kamar Kidal ya farfado da farin jinin gwamnatin a zukatan jama’ar Bamako.
Cikin abubuwan da suka faru bayan harin, mun ga yadda aka kama wasu mutane da zargin hannunsu, da kuma wani mutum aka kona da ransa a kan titi.