Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Uba Sani, ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin da aka kai a cocin Fadan Kamatan- Katolika na Kafanchan, da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Da yake nuna bacin ransa game da harin a ranar 8 ga watan Satumba wanda ya yi sanadin asarar rayuka, Gwamnan ya sha alwashin zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aikin tare da tabbatar da cewa sun fuskanci tsantsar fushin doka. Ya ce an kai harin ne da nufin tayar da rikicin kabilanci da addini a jihar Kaduna da kuma zagon kasa ga kokarin gwamnati na sake dawo da aminci tsakanin al’ummar jihar.
Gwamna Uba Sani ya bukaci jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da kama wadanda ke da hannu cikin kai harin.
Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su tare da ba su tabbacin cewa, gwamnatin jihar za ta tallafa musu kan wannan mawuyaciyar rayuwa da ake ciki a wannan lokaci.
Gwamnatin Gwamna Uba Sani ta dauki kwararan matakai na maido da zaman lafiya a cikin al’ummomin da ke fama da rikici ta hanyar karfafa hadin guiwa da Hukumomin Tsaro na Tarayya da kuma karfafa hukumar ‘yan banga ta Kaduna (KADVS). Kwanan nan ne gwamnatin jihar ta dauki sabbin jami’an tsaro na ‘yan banga 7,000 tare da horar da su.
Gwamnatin Kaduna ta kuma gudanar da muhimman tsare-tsare kan harkokin tsaro inda ta tattauna da manyan jami’an gwamnatin tarayya da ke da alhakin tsaro kamar ministan harkokin ‘yansanda, Sanata Ibrahim Geidam; Karamin ministan harkokin ‘yansanda, Hon. Imaan Sulaiman-Ibrahim da shugabannin tsaro da aka nada kwanan nan.