Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta cafko wadanda suka kai munanan hare-hare da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama a kananan hukumomin Barkin Ladi da Bokkos na jihar Filato.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarci al’ummomin da harin ya shafa a jihar Filato domin jajantawa jama’a da gwamnatin jihar kan kashe-kashen da aka yi.
- Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Na’Abba
- Bikin Kirsimeti: Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da Hare-haren Filato
Da yake shan alwashin cewa dole ne a dakatar da kashe-kashen da ake yi a Filato da sauran sassan kasar, Mataimakin Shugaban a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Stanley Nwocha ya fitar ya ce, “Muna fatan za ku karbi ta’aziyyarmu. Muna ma su ba ku hakuri, domin ba za mu huta ba, har sai an cafko wadanda suka aikata wannan mummunan lamari kuma an hakunta su”.
Shettima ya kara bayyana wa Al’ummar Jihar matukar damuwar da Shugaba Tinubu ke ciki tun lokacin da ya samu labarin faruwar lamarin, inda ya ce shugaban kasa ya girgiza matuka da wannan bala’i da ya toshe murnar bikin Kirsimeti da kasar ke ciki.