Hukumar Jiragen kasa ta Nijeriya ta sanar da cewa, ta yi asarar sama da Naira Miliyan 531 na tikitin shiga Jirgin daga Abuja zuwa Kaduna acikin watanni biyar da suka gabata, sabida dakatar da zirga-zirgar Jiragen.Â
In za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Maris na 2022 ne, ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasan hari a dajin Kaduna, inda suka sace Fasinjojin Jirgin da dama wadanda suka taso daga Abuja zuwa Kaduna.
Shugaban hukumar na kasa, Fidet Okhiria ne ya sanar da hakan a jiya Laraba a taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke a jihar Legas.
Ya bayyana cewa, asarar an yi ta ne daga ranar 28 ga watan Maris zuwa ranar 28 ga watan Agusta, inda kuma ya nuna takaicinsa, kan cewa har yanzu ‘yan bindigar na cigaba da rike wasu fasinjojin, ciki har da wasu ma’aikatan hukumar.
Ya sanar da cewa, Gwamnatin Tarayya na yin dukkan mai yiwuwa don ganin an kubutar da su daga tarkon ‘yan bindigar.