Wasu dangi daya su shida da Wani Daya dake tsare a hannun ‘yan bindigan da suka kaiwa fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja hari a ranar 28 ga Watan Maris, 2022 sun shaki iskar ‘yan ci bayan da fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya shiga tsakani.
Gumi ya tuntubi wadanda suka yi garkuwa da su ta hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Malam Tukur Mamu, inda ya roke su da su sako yaran daga hannun su.
An ce ya aika musu da nasihohi a hudubar shi yana mai magiya da rokon ‘yan ta’addan da su yi la’akari da sakin ‘ya’yan talakawa da iyayensu da ba su ji ba ba su gani ba.
An tabbatar da cewa, lafiyar biyu daga cikin yaran ta tabarbare tun bayan sakin Wani bidiyo da ‘yan ta’addan suka fitar a kwanakin baya suna yiwa mahaifansu bulala.
Acewar Mai taimaka wa Malamin a fannin yada labarai, a wata sanarwa da ya fitar, Mamu yace “Sakamakon haka, an sake sakin wasu karin mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a cikin fasinjojin jirgin a safiyar Laraba bayan Gumi da wani dan majalisar tarayya da ba a bayyana sunansa ba sun shiga tsakani.
Wata sanarwa da Mamu ya sanyawa hannu a ranar Laraba da yamma, wacce aka aikewa LEADERSHIP da kwafinta, ta tabbatar da sakin iyali su shida ( Uwa da Uba da yara Hudu) da wani fasinja daya.