Tawagar ‘yan majalisar wakilai na Arewa ta yi alkawarin bayar da naira miliyan 350 don sake gina kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna da harin bam ya rutsa da su.
Shugaban tawagar, Alhassan Ado Doguwa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar a wata ziyarar jaje da suka kai gidan Gwamnatin Kaduna a ranar Litinin.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Asibiti, Makaranta Da Gidaje Ga Al’ummar Tudun Biri – Gwamnan Kaduna
- Gobarar Da Ta Tashi A Tsibirin Maui Ta Bata Amincewar Da Jama’a Suka Yi Da Gwamnatin Amurka
Doguwa ya sanar da cewa, tallafin kari ne kan Naira miliyan 45 da tawagar ‘yan majalisar da ke wakiltar jihar a majalisar wakilai suka bayar tun farko ga wadanda lamarin ya shafa.
Da yake magana kan yadda za a kashe kudin da suka bayar, ya ce, za a gina Makaranta, Asibiti, ofishin ‘yansanda, rijiyar burtsatse ta zamani mai amfani da hasken rana da dai sauransu.
Doguwa ya kuma bayyana cewa, wasu Uku daga cikin ‘yan Majalisar wakilai na Kudancin Nijeriya sun tallafa da kudi naira miliyan 30.
Doguwa ya yabawa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Tinubu bisa gaggauta kai agaji ga wadanda abin ya shafa da kuma kula da jin dadin wadanda abin ya shafa.
.A asibitin koyarwa na Barau Dikko, inda ‘yan majalisar suka duba lafiyar wadanda suka jikkata, Doguwa ya bayar da tallafin kudi naira miliyan daya ga majinyatan.
A nasa jawabin, gwamnan jihar, Sanata Uba Sani, ya bukaci ‘yan majalisar da su tabbatar da cewa, an bi wa wadanda lamarin ya shafa hakkinsu kuma a yi musu adalci ta hanyar tabbatar da cewa an binciki lamarin, domin zakulo wadanda suka aikata laifin.