Sakamakon wani harin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi a kan jami’an tsaro, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaron su kimanin ashirin da biyar, wanda ya hada da jami’an soja ashirin da daya da kuma ‘yan banga hudu a Kundu da ke Karamar Hukumar Rafi, kan iyaka da Karamar Hukumar Wushishi.Hakan ya sa jama’a ke ganin akwai bukatar gwamnati ta sauya fasalin yadda aikin ke gudana a halin yanzu.
Lamarin ya faru ne a daren lahadi, inda rahotanni suka tabbatar da cewa, jami’an tsaron sun samu labarin zuwan ‘yan bindigar tafe da shanu da kuma tumakan da suka sato a kan hanyar su ta tsallakawa zuwa sansaninsu.
Jami’an tsaron sun yi kokarin yi wa ‘yan bindigar tara-tara, ba su yi aune ba sai ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna; suka yi ta faman ba-ta-kashi, inda wasu rahotanni suka shaida cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kashe sama da ‘yan bindiga hamsin, yayin da ‘yan bindigar kamar yadda rahotanni suka bayyana sun hallaka jami’an tsaron su kimanin ashirin da biyar, cikin su har da mai mukamin Kanal da Manjo da kuma ‘Yan Banga guda hudu.
A safiyar Litinin ne Gwamnan Jihar Neja, Hon. Umar Mohammed Bago ya ziyarci Shugaban Rundunar Sojan Nijeriya, inda ya bayyana masa matsalolin da jihar ke fuskanta tare da neman Rundunar ta kara kaimi a kan wanda take yi a halin yanzu da kuma ba da tabbacin gwamnatin tasa a shirye take wajen kara karfafa wa Rundunar gwiwa tare da goya mata baya don kawo karshen matsalolin tsaro a fadin jihar Neja.
Kazalika, gwamnan ya alakanta ta’azzarar matsalar tsaron da yawan fadin kasa da jihar ke da ita, domin a cewar tasa ta fi dukkanin sauran Jihohin Kasar nan yawan fadin kasa da iyakoki, kama daga Jihar Zamfara, Kebbi, Katsina da kuma Kaduna; inda mafi yawan ‘yan bindigar ke da matsugunai.
A lokacin da gwamnan ke wannan jawabi ga Shugaban Rundunar Sojan, Janar Christopher Gwabin Musa, ya bayyana cewa jihar tasa na kewaye ne da manya-mayan rafuka da ke baiwa Sojojin matukar wahala wajen gudanar da ayyukansu yadda ya dace.