Rundunar ‘yansandan Nijeriya da ke jihar Kebbi, ta kwato wani makamin roka guda daya da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi watsi da su a kauyen Dan-Umaru da ke gundumar Bena a karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar.
Bayan samun rahoton kai harin ‘yan bindigar a kauyen, tawagar ‘yansanda da ke garin Dan-Umaru, suka mayar da martani cikin gaggawa tare inda suka yi musu ruwan harsashi har ta kaiga an sha karfin su.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Samuel Titus Musa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata a Birnin Kebbi, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a hedikwatar rundunar jihar ga manema labarai.
Kwamishinan ya ce “tawagar ‘yansandan sun yi nasarar dakile harin tare da gano makamin roka guda daya, da ‘yan bindigar da ake zargin suka tsere da raunukan harbin bindiga daban-daban”
Bisa ga hakan ya yi kira ga jama’a a fadin jihar da su taimaka wa ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro wajen ba da muhimman bayanai na duk wani motsi ko aiki da ake zargin laifi ne. “Domin ta hanyar bayar da bayai ne za mu iya yin aikin namu kamar yadda doka ta tana da na dakile duk wani laifi”, inji Shi.