Zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD ta shirya harkar murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa a daren ranar Juma’a a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka.
Mukaddashin babban sakatare janar na MDD kuma babban wakilin kawancen wayewar kan al’umma ta MDD Miguel Angel Moratinos, ya ce sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa shekara ce ta maciji, wadda ke da alaka da hikima, taka-tsantsan da dabaru, kuma tana nuni da sauyi da samun ci gaba.
- Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
- Shugaban Kasar Sin Ya Mika Gaisuwar Sabuwar Shekara Ga Dukkan Jami’an Tsaro
Moratinos ya kara da cewa, “Tare da dimbin kalubalen da duniya ke fuskanta, ruhin da ke cikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar Sinawa ya kasance kamar fitilar dake ba da haske ga bege da kyakkyawan fata.”
A nasa bangare, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya bayyana fatansa na samun zaman lafiya da wadata da jituwa a sabuwar shekara mai zuwa bisa kalandar gargajiyar Sinawa.
Fu ya kara da cewa, yayin da jama’a ke bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD a bana, an shiga tsaka mai wuya kan makomar mulkin duniya, kasar Sin na ci gaba da yin kokari tare da kasashen duniya wajen tabbatar da zaman lafiya da wadata da makoma mai kyau ga kowa da kowa. (Mohammed Yahaya)