Taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin (CPPCC) da za a fara ranar 4 ga watan Maris, da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da za a fara ranar 5 ga watan Maris, su kasance manyan taruka biyu na kasar Sin inda ake gangamin siyasa domin nazartar baya da kuma hangen gaba. Wadannan hukumomi biyu suna karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda ke karkashin jagorancin babban sakataren Xi Jinping. Kwamitin CPPCC na kasa, mai mambobi 2,169, yana aiki ne a matsayin babbar hukumar da ke tafiyar da tsarin dunkulewar sassan kasar ta fuskar siyasa, wanda ke hada kungiyoyin zamantakewa daban daban mashawarta jam’iyyar. Ita kuma, majalisar NPC mai wakilai 2,977, tana aiki ne a matsayin majalisa guda, kuma babbar majalisar dokokin kasar.
Hasashen manazarta kan taruka na bana na da alaka da wani taron karawa juna sani wato “taro kan kamfanoni masu zaman kansu” wanda shugaba Xi ya karbi bakunci a ranar 17 ga watan Fabrairu, wanda ya samu halartar manyan ’yan kasuwa na kasar. A shekarar 2018 ne aka fara gudanar da irin wannan taro da ya kasance na musamman wanda ke kara wa tattalin arzikin kasar karfin gwiwa, musamman bayan dawowar shugaba Trump na Amurka a karo na biyu, wanda ya ayyana kansa a matsayin “sarkin kakaba haraji”, wanda tuni ya sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin Sin da ke shiga kasarsa. Yanzu, hankalin mahukunta ya karkata kan yadda Sin za ta kara kuzari, da tallafawa kasuwanci da kamfanoni, da kuma mayar da martani ga manufofin cinikayya na Trump.
Ana sa ran tarukan biyu za su bayyana ajandar da za ta kara habaka ci gaba idan aka kwatanta da bara, tare da hasashen kusan kashi 5% na ci gaban GDP, da kashi 4% na GDP na gibin kasafin kudi, da kashi 2% na hauhawar farashin kayayyaki. Bugu da kari, ana sa ran za a samu karin lamuni na kusan yuan tiriliyan 3 daga asusun baitulmali na musamman da kuma yuan tiriliyan 4.5—-5 daga lamuni na musamman na kananan hukumomi. Ta hakan za a gabatar da matakan da za su bunkasa sayayya da karfafa kamfanoni cikin gida masu zaman kansu a fannin kirkire-kirkire. Kazalika, ana sa ran za a tabo batutuwan da suka shafi ci gaban kamfanonin waje masu zaman kansu, da manufofin kasashen wajen musamman wadanda suka shafi batun Taiwan da yadda za a mayar da martani ga hauragiyar Trump. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp