• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hasashen Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-kwana

by Shehu Yahaya and Sulaiman
1 month ago
Ambaliyar ruwa

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bukaci daukacin Al’ummar jihar da su kasance cikin shiri sakamakon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) suka bayar, inda suka nuna yiyuwar samun guguwar iska da ruwan sama mai yawa a faɗin jihar daga ranar Laraba, 10 zuwa Litinin, 15 ga Satumba, 2025.

A wata Sanarwar manema labarai wadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da Kula da Bala’o’i ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta fitar, ta jaddada hatsarin da hakan zai iya haifarwa kamar ambaliya, cika titi da ruwa a cikin birane, ƙaruwa a matakin koguna, da kuma yiwuwar asarar dukiya, amfanin gona da ababen more rayuwa.

  • Gwamnan Kebbi Ya Dakatar da Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya Biyo Bayan Sakaci A Aiki

Kwamishinan yada labaran jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa gwamnati ta sanya dukkan hukumomin da suka dace cikin shirin ko-ta-kwana domin kare rayuka da dukiyun jama’a.

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

“Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki.

Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar.

“Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba da Alhamis. Muna roƙon jama’a da su guji fita ba dole ba yayin ruwan sama mai ƙarfi, su daina ƙoƙarin tuƙi cikin hanyoyin da ruwa ya mamaye, sannan su nisantar da yara daga guraren da ruwa ke taruwa. Manoma kuma su gaggauta ɗaukar matakan kare amfanin gona da wuraren ajiya,” in ji Dakta Mazadu.

“Mun tura tawagar gaggawa zuwa shiyyoyi daban-daban, kuma ana ƙarfafa gwiwar jama’a da su rika hanzarta bayar da rahoton duk wani lamari na ambaliya ko wata gaggawa da ke barazana ga rayuka ta hanyar amfani da layukan gaggawa na hukuma na KADSEMA,” in ji shi.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa amma a kasance cikin shiri, tana mai jaddada bukatar haɗin kan al’umma wajen rage haɗurran da ke tattare da yanayin da ake sa ran zai faru.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki
Labarai

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 
Labarai

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja
Labarai

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Next Post
Duniya Za Ta Ci Karin Gajiya Daga Karfafuwar Hadin Gwiwar BRICS 

Duniya Za Ta Ci Karin Gajiya Daga Karfafuwar Hadin Gwiwar BRICS 

LABARAI MASU NASABA

Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.