Binciken farko da Gwamnatin tarayya ta yi game da sakin layin da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya yi a makon da ya gabata, ya nuna cewa, babu batun zagon-kasa ga harkokin sufurin jiragen.
Ministan Sufuri, Saidu Ahmed Alkali ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati a karshen mako, tare da Babban Darakta na Hukumar Jiragen Kasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa.
Alkali ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike kan hatsarin amma ya jaddada cewa, binciken farko ya nuna babu wani batun zagon kasa.
Ya tabbatar da cewa, an kwashe dukkan fasinjoji 618 da ke cikin jirgin cikin koshin lafiya. 20 sun samu kananan raunuka, yayin da bakwai ke kwance a asibiti amma tuni an sallame su, kuma NRC ce ta dauki nauyin biyan kudaden kiwon lafiyarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp