Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana matukar kaduwarta kan hatsarin da ya faru da jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, wanda ya afku a safiyar ranar Talata, wanda ya haifar da firgici a tsakanin fasinjoji da iyalansu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar ranar Talata a Kaduna.
- Sassou Nguesso: Muna Fatan Gaggauta Tabbatar Da Sakamakon Taron Beijing Na FOCAC
- Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Ya Yi Hatsari, Ba A San Halin Da Fasinjoji Ke Ciki Ba
Maiyaki ya kara da cewa, bayan rahoton faruwar lamarin, Gwamna Uba Sani nan take ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) da Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar da su gaggauta kai dauki ga fasinjojin da lamarin ya rutsa da su.
Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.
“Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari, duk wanda ya samu rauni za a kula da shi cikin gaggawa, yayin da ake ba da tallafin gaggawa na psycho-socio da tallafin likita ga wadanda abin ya shafa,” in ji Maiyaki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na sanya ido sosai kan lamarin tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya da masu ruwa da tsaki da abin ya shafa.
Da safiyar ranar Talata ne muka rahoto muku cewa, jirgin kasa da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ya sauka a kan layin dogo jim kadan bayan ya bar tasharsa da misalin karfe 11 na safe, inda ya bar fasinjojinsa cikin firgici.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp