Mutane 13 sun rasa rayukansu, ciki har da sojin ruwa, a wani hatsarin kwale-kwale a kan hanyarsu ta zuwa tsibirin Elephanta, wajen yawon buÉ—e ido da ke birnin Mumbai, a Indiya.
Kwale-kwalen ya kife bayan ya yi karo da wani jirgin sojin ruwa, inda ya haifar da turmutsitsi.
- Manufar Sin Ta Yada Zango Ba Tare Da Biza Ba Ta Kara Jawo Hankalin Masu Yawon Shakatawa Na Ketare
- Da Dumi-Dumi: An Yi Kutse A Shafin Hukumar Kididdiga Ta Kasa
Rahotanni sun ce sama da mutane 80 ne ke cikin kwale-kwalen yayin da lamarin ya afku.
Masu gadin teku da ‘yansandan ruwa suna ci gaba da aikin ceto, inda suke jigilar waÉ—anda suka tsira zuwa asibiti mafi kusa domin samun kulawa.
Ana kuma ci gaba da neman sauran waÉ—anda hatsarin ya rutsa da su.