Akalla mutune 12 ne suka rasa rayukansu a hatsarin Kwale-kwale a kogin Kungra Kamfani a Arikiya da ke karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa.Â
An tattaro cewa mutum 19 ne suka kasance fasinjojin da ke cikin jirgin Kwale-kwalen a lokacin da ta yi hatsarin.
- Tarihi Zai Dorawa Japan Alhakin Sakin Gurbataccen Ruwan Nukiliya Zuwa Teku
- Badaru Na Da Kwarewar Jagorantar Ma’aikatar Tsaro – ANA
Direbobi sun ceto mutum bakwai daga cikin fasinjojin, yayin da sauran suka rigamu gidan gaskiya.
Bayanin faruwar lamarin ya fito ne daga bakin kakakin majalisar jihar, Ibrahim Balarabe Abdullahi a yayin zaman gaggawa da ta gudanar a ranar Alhamis.
“Cikin bakin ciki mun rasa mutum 12, da suka hada da maza da mata a hatsarin jirgin ruwa a Arikiya, karamar hukumar Lafia.
“Mutane 19 ne suke cikin jirgin Kwale-kwalen, 12 sun mutu, an ceto 7. Karamar hukumar Lafia da jihar mu sun shiga alhinin faruwar wannan hatsarin,” ya shaida.
Kakakin a madadin illahirin mambobin majalisar, ya jajanta wa gwamnatin jihar, karamar hukumar Lafia da iyalan mamatan bisa wannan hatsarin.
Ya yi addu’ar Allah bai wa iyalan mamatan hakurin juriyar rashin masoyansu da suka yi.
Kakakin ya yi addu’ar Allah ya jikansu ya gafarta musu kurakuransu kana ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya.
Daga bisani mambobin majalisar suka yi shiru na ‘yan mintuna domin alhinin mamatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp