An tabbatar da mutuwar mutane 37 a wani hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da wasu takwas kuma sun samu raunuka.
Babban jami’in hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), shiyya ta 12 da ta kunshi jihohin Bauchi, Borno da Yobe, ACM Rotimi Adeleye, ne ya tabbatar wa manema labarai afkuwar hatsarin a ranar Talata.
Adeleye ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Talata a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu kusa da wani kauye mai suna Jakana wanda ya hada da motoci uku – Homa bas guda biyu da kuma Golf salun guda 1.
Ya bayyana cewa motocin bas guda biyun ne suka yi karo da juna inda nan take suka kama da wuta, mutane 37 suka mutu nan take saboda konewar, ba a iya gane mutanan.
Hukumar FRSC ta tura jami’anta domin aikin ceto inda suka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno domin samun umarnin kotu na binne wadanda suka rasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp