Nijeriya na cikin wani mawuyacin hali, inda take fama da kalubale masu alaka da juna; wadanda suka shafi manufofin kasashen waje, samar da danyen man fetur da sayar da shi da kuma faduwar darajar Naira a kan kudaden kasashen waje da ke barazana ga zaman lafiyarta da ci gabanta. Ko shakka babu, wannan yana nuni ne da rashin iya gudanar da aiki da hangen nesa na masu jagoranci a kasar.
Tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya, na bukatar fahimtar kasar da kuma su kansu‘yan kasar tare da bukatar sabbin hanyoyin magance hauhawar farashin dala; wanda zai taimaka wa al’umma wajen samun kwanciyar hankali da wadata.
Me ya sa Nijeriya ta samu kanta a cikin wannan hali, sannan kuma wane ne zai iya ceto ta daga wannan kangi?
A kakar zaben 2023, an ta faman yin hayaniya game da wanda ya fi cancanta a zaba, inda jam’iyya mai mulki ta damu jama’a da shelar cewa, “A bi wadanda suka san hanya”, to yanzu ‘yan Nijeriya sun gane cewa; jam’iyya mai mulki ta kai wannan kasa cikin ramin kura, wanda mai tsawon rai ne kadai zai iya ganin badi.
A takaice, don samun damar magance wannan matsala; ana bukatar shugaba mai hangen nesa, wanda kuma ya san kalubalen Nijeriya.
Wa Ke Bukatar Dala?
A nan kashi biyu ne, wato hukumomin da alhakinsu ne tabbatar da cewa; Naira ba ta fadi kasa warwas ba, sun bayar da nasu dalilan. Domin ilmanatar da al’umma, bari mu yi nazarin wadannan dalilai biyu kamar haka:
i. Labarin da aka bai wa ‘yan Nijeriya a hukumance shi ne, karuwar bukatun ta samo asali ne sakamakon yawan bukatar dala, don biyan kudin makaranta, biyan kudin dala; domin neman lafiya, raguwar kudaden ajiyar waje, ficewar masu sa hannun jari ‘yan kasashen waje (FPI), da kuma satar man fetur.
ii. Bayanai da Nazari na nuni ne da cewa, hauhawar farashin dala ta samo asali ne sakamakon gazawar Babban Bankin Nijeriya (CBN), wajen biyan bukatun kamfanoni da sauran jama’a da rashin dawo da kudaden da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya sayar, makudan kudaden shiga wanda gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi ke samu daga kwamitin rabon kudin shiga na tarayya ke bayarwa (FAAC), wanda wasu ke karewa a sayen dalolin da ake boyewa, wanda jami’an gwamnati da sauran mutane ke yi tare da salon da babban bankin kasa ya dauka na amfani da tsarin gudanar da tattalin arzikin da bai dace da Nijeriya ko kadan ba, bai kuma dace da zamanin da muke ciki a halin yanzu ba.
Shin Babban Bankin Nijeriya Da Ma’aikatar Kudi Ta Tarayya Da Kwamitin Gyaran Haraji Na Shugaban Kasa Za Su Iya Ceto Naira Kuwa?
Mutanen da Shugaban kasa ya zaba, a cikin butulcinsu da rashin kishin Nijeriya da hangen nesa tare da kwadayin tabbatar da su a kan madafun iko, ya sa suka yanke shawarar samar da hanyoyin shigar kudin gwamnati da samar da hanyoyin samun kudaden haraji, wadanda ba su dace da yanayin da Nijeriya ta samu kanta a ciki ba. Bayan haka kuma, sun kasa yin la’akari da halin da talakawa ke ciki, wanda tarihin wadannan kura-kurai sun samo asali ne daga:
1- Lokacin Korona: An rage darajar Naira sau shurin masaki tsakanin 2020 zuwa 2021 daga kimanin Naira 306 zuwa Naira 360 a duk dalar Amurka daya da kuma daga Naira 360 zuwa kusan N381a kan duk dala daya, sannan kuma daga N381 zuwa kusan N410 na dala daya. Wannan zaluncin karya darajar Naira, ya faru ne a lokacin da aka dakatar da duk wasu hada-hada da zirga-zirga da kuma cinikayya tare da ayyukan tattalin arziki a duniya baki-daya.
2- Dakatar da Sayar da kudaden waje (FORED) ga ‘yan canji na ‘Bureau De Change’, da kuma rage yawan bayar da dala ‘FORED’ na mako-mako ga bankunan kasuwanci, wanda bankin CBN ke yi, ya haifar da karanci tare da kara matsin lamba ga darajar Naira.
3- Burin bankin CBN na samun dalar Amurka biliyan 200, ta hanyar shigar kudaden waje zuwa gida. (Tsarin RT200 FD): Shiri ne wanda aka kaddamar a shekarar 2022 da nufin inganta shigo da kudaden waje, ba ta hanyar fitar da ko sai da man fetur ba.
4- Sanarwa: Rashin tabbas a kasuwar canji, ya yi kamari bayan sanar da cewa an saki Naira ta nemar wa kanta daraja a kasuwar canji da rugujewar tsarin canjin kudi; kwanaki kadan bayan rantsar da shugaban kasa.
5- Shuwagabanin bankin CBN, hukumar kwastan da sauransu a kokarinsu na tabbatar da shugabancin hukumominsu daban-daban, maimakon samar da kwanciyar hankali ta fuskar gina turbar da za ta fitar da Nijeriya daga wannan yanayi, sai suka gwammace su rungumi hanyar samo wa gwamnati hanyoyin shigar kudi. Wannan yanayi ya haifar da asara mai dimbin yawa tare da tabarbarewar canjin kudi da faduwar darajar Naira da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
6- Hana sayarwa tare da bayar da kudin guzuri na ‘PTA da BTA’, a tsabar takardun kudi.
7- Hana ‘Payoneer da World Remit’ da sauransu wajen hada-hada da kuma turo da dala zuwa Nijeriya.
8- Cire kason riba na kashi 2.5 cikin 100 a kan kowace dala a kasuwancin ‘FORED’ na tsakanin Bankuna.
9- Gaggawar neman nasara na kwamitin tsarin kudi na Shugaban kasa da gyara haraji: Wani abun mamaki shi ne, yadda wannan kwamiti ya ba da shawarar sanya haraji a kan hada-hadar kudaden waje, inda kasuwar za ta dora nauyin ne kawai ga mai saye, yayin da mai sayen zai mai da nauyin a kan talakawan Nijeriya ko kuma kara dankwafar da tattalin arzikin kasa tare da kara yi masa zagon kasa.
10- Ziyarar bazata da jami’an EFCC da Kwastam suka yi zuwa kasuwanin kudaden waje na bayan fage da bindigogi: Shin wannan barazanar za ta ceto Naira kuwa?
11- Daftarin bayyanai na ka’idoji da sharuddan kula wa da kasuwancin BDCs: Binciken farko na daftarin na nuna shakku a kan ingancinsa.
12- Ci gaba da sakin dala 20,000 na mako-mako ga BDCs: Shin wannan canjin yanayin zai zama maganin matsalar? Mu jira mu gani.
Mu Kai Ziyara:
A- Bayanan Yanayin Canjin Kudaden Duniya Na Dandalin Stebe Hanke:
Ya wallafa a shafinsa na Twitter (D), a ranar 3 ga Yuni 2023, inda ya yi bayanin tabarbarewar Naira a takaice.
“Yayin da Buhari ke mika karagar cin hanci na mulki ga Shugaban Kasa Tinubu, tattalin arzikin Nijeriya na cigaba da tabarbarewa. ’Currency Watchlist’ na Hanke na wannan makon, na nuni da cewa, Nijeriya ce a matsayin lamba ta 20. Naira ta ragu da kashi 26 cikin 100, idan aka kwatanta ta da dalar Amurka daga ranar 1 ga Janairun 2022: wannan kudin ya zama kudin bola, inda Naira 770 ke daidai da dala daya tak; a ranar 26 ga Mayun 2023.
B- Musanya Tsaro Na Kasuwancin Kasuwanci (FMDK):
Wannan shi ne zauren kasuwanci na ‘FORED’ da bankin CBN ya gamsu da shi.
A ranar 21 ga Fabrairu, 2024, Wannan kasuwar canjin kasashen waje mai cin gashin kansa (NAFED), ana sayar da Naira 1551.90 a kan dala daya, yayin da kasuwar musayar kudaden waje na Nijeriya (NAFEM), ya rufe a kan Naira 1542.58 duk dalar Amurka guda.
Ita kuma kasuwar bayan fage ta ranar, ta kasance duk dala daya ana sayar da ita a kan Naira 1,600.00.
C- Kasashe Goma Mafi Rauni A Afirka Kan Kudin Dala
Bayanai daga ‘Google Finance’, da bayanai daga ‘Forbes Currency Conberter’ na ranar 12 ga Fabrairun 2024, ‘Business Insider Africa’, ya nuna Nijeriya ce a matsayi ta 10 tare da São Tomé da Principe a 1st, Kasar Saliyo ta 2, Kasar Malawi kuma a matsayi ta 9.
A karshe
Magance faduwar darajar Naira, na bukatar tsari iri daban-daban; amma ko shakka babu, babu wanda ake bi a halin yanzu, Nijeriya na bukatar jagoranci mai hangen nesa; wanda zai wuce gaba, domin samo mafita ga kasar baki-daya.
Lallai Nijeriya na cikin tsaka-mai-wuya, sannan makomarta ta dogara ne da irin zabin shugabanta da kuma ‘yan kasar suka yi ko za su yi.
Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna