Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta ragu zuwa kashi 16.05% a watan Oktoba, saɓanin 18.02% yadda yake a watan Satumba na 2025.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta rahoto cewa, adadin ya ragu da kashi 1.96% idan aka kwatanta da karuwar farashin kayayyaki a watan Satumba na 2025.
ADVERTISEMENT
A halin yanzu, karuwar farashin kayayyaki a watan Oktoba na 2025 ta ragu da kashi 13.12% idan aka kwatanta da wannan watan a shekarar da ta gabata.
An samu wannan raguwar ne sakamakon sauye-sauyen da aka samu a shekarar da muke ciki.













