Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya a watan Yulin 2023 ya karu zuwa kashi 24.08 cikin 100 idan aka kwatanta da kashi 22.79 da aka samu a watan Yunin 2023.
Alkaluman na baya-bayan nan dai ya karu da kashi 1.29 bisa 100 daga alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a watan Yunin 2023.
- Ganduje Ya Bukaci ‘Yan Majalisar Dokokin APC Su Goya Wa Abba Baya
- Gwamna Lawal Ya Gana Da Hafsan Sojin Kasa Kan Matsalar Tsaro A Zamfara
Haka zalika, a duk shekara, hauhawar farashin kayayyaki na karuwa inda ya kai kashi 4.44 bisa dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Yulin 2022, wanda ya kai kashi 19.64 bisa 100 ga sabon alkaluman da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar.
An danganta karin na watan Yuli 2023 da tashin farashin man fetur da kuma dalar Amurka.
Karuwar farashin ya danganci abinci, abubuwan sha, gidaje, ruwa, wutar lantarki, gas da sauransu.
Haka zalika, hauhawar farashin kayan abinci a watan Yulin 2023 ya karu zuwa kashi 3.45 cikin dari, wannan ya kai kashi 1.06 bisa dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Yunin 2023 (kashi 2.40).