Mataimakin shugaban kungiyar yada harshen larabci ta duniya, Farfesa Muhammad Rabiu Auwal Sa’ad ya bayyana cewa Hausawa da ke waka da Larabci za su wakilci Nijeriya a taron baje kolin nuna fasahar sarrafa harshen Larabci na duniya da wake-wake na Larabci wanda za a gudanar a garin Sharika da ke kasar Dubai a wannan shekarar.
Farfesa Muhammad Sa’ad wanda ya kasance shugaban sashin koyar da larabci na jami’ar Bayero da ke Kano, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen bude taron kungiyoyin matasa da cibiyoyi masu wakokin larabci da suka zo daga jihohin kasar nan.
Ya ce an zabo wakilai 10 daga jihohi wadanda suka hada da Kano da aka dauki mutum bakwai, sai kuma wakilai daga Borno, Kwara, Sakwato da kuma Jigawa, inda wasu ba za su samu halatta ba, sakamakon wasu dalilai da suka bayar na uzuri da ya hana su.
Farfesa Sa’ad ya bayyana a wannan jawabi a wajen taron wanda shi ne irinsa na farko da aka taba shirya a Nijeriya, kuma kasashen Afirka bakwai ne za su fafata a wannan taron share fage da zai gudana a garin Kano a cikin wannan mako.
Shi ma babban jami’in mai kula da sashen koyar da larabci da yada shi a Nijeriya, Dakta Umar ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da Nijeriya ta samu dama na shiga taron baje koli a wannan shekara da nufin zakulo matasan masu fasaha da hazaka a wajen iya sarrafa harshen larabci, kasancewar kasashen Larabawa ba su da cikakkiyar masaniya na yadda Allah ya a zurta matasan Nijeriya wajen sarrafa harshen Larabci.