Mataimakiyar shugaban kula al’amuran daliban na jami’ar Capital City (CCU), Dakta Salwa Shehu Dawaki ta bayyana cewa daya daga cikin manyan jami’o’i da ke Kano na shirin zakulo hazikan dalibai ‘yan asalin Jihar Kano, domin ba su gurbin karatu kyau a matsayin gudummawa da karfafa gwiwa ga hazikan dalibai, domin tallafa wa kokarin gwamnatin Kano na bunkasa ilimi.
Dakta Salwa ta bayyana hakan ne a lokacin da take jawabi a wajen bikin baja kolin al’adun gargajiya da aka shirya wa sababbin daliban da aka rantsar a jami’ar CCU.
Ta ce wannan bikin al’adun ga daliban ya shafi nuna sutura da yadda kabilu daban-daban da ke kasar nan na tsarin rayuwarsu da shugabancin wanda ya hada da Fulani, Yaroba, Hausawa, Ebo da Barebari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp