Hedikwatar tsaro ta Nijeriya a ranar Litinin ta ayyana neman ‘yan ta’adda 19 ruwa a jallo da suka addabi jihar Katsina da makwabtanta.
Hedikwatar tsaron ta kuma sanar da bayar da tukuicin Naira miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga cafke daya daga cikin wanda ake neman ruwa a jallo.
Sunayen ‘yan ta’adda 19 da hedkwatar tsaron Nijeriya ta bayyana a matsayin wanda take nema ruwa a jallo a ranar Litinin sun hada da:
“Sani Dangote daga Zurmi, jihar Zamfara; Bello Turji Gudda daga Fakai, jihar Zamfara; Leko daga Matazu, jihar Katsina; Dogo Nahali daga Kankara, jihar Katsina.
“Halilu Sububu daga Maradun, jihar Zamfara; Nagona daga Isa, jihar Sokoto; Nasanda daga Zurmi, jihar Zamara; Isiya Kwashen Garwa daga Faskari, Jihar Katsina.
“Ali Kachalla wanda akafi sani da Ali Kawaje daga Dansadau Maru, jihar Zamfara; Abu Radde daga Batsari, jihar Katsina; Dan-Da daga Batsari, jihar Katsina; Sani Gurgu daga Batsari, jihar Katsina.
“Umaru Dan Nijeriya daga Mada, jihar Zamfara; Nagala daga Maru, jihar Zamfara; Alhaji Ado Aliero daga ‘Yankuzo Tsafe, jihar Zamfara.”
Sauran sun hada da “Monore daga ‘Yantumaki, jihar Katsina; Gwaska Dankarami daga Zuri, jihar Zamfara; Baleri daga Shinkafi, jihar Zamfara; Mamudu Tainange daga Batsari, jihar Katsina.”
Hedikwatar tsaron ta kuma bukaci duk wanda yake da bayanin yadda za a zakulo wadanda ake zargin da ya kira: 0913 590 4467.
Har ila yau, a cikin ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, akwai Ado Aleru, wanda aka baiwa sarautar Sarkin Fulanin Zamfara kimanin watanni hudu da suka gabata.