Hedikwatar tsaro ta karyata rahoton da ke cewa shugaban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya rasu.
Da safiyar ranar Talata ne wasu kamfanin jaridu suka buga wani rahoton karya da ke cewa, Janar Musa ya rasu.
- Zaben Nasarawa: ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaro Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Me Ya Sa Za A Sake Zabar Kasar Sin?
A wani martani na hanzari da Hedikwatar tsaro ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa, Babban Hafsan Tsaro yana raye kuma cikin koshin lafiya.
In ba a manta ba dai, Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Janar Musa a matsayin babban hafsan tsaro a ranar 19 ga watan Yunin 2023.