Jami’an hukumar Hisbah reshen jihar Kano sun cafke wasu matasa 19 a wata shahararriyar cibiyar taro don daura wa wasu samari biyu auren luwadi.
Matasan ‘yan kimanin shekaru ashirin da haihuwa an ce sun taru ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin ‘yan luwadi ne, Abba da Mujahid.
Jami’an Hisbah da ke hedikwatar hukumar da ke Sharada, Kano, sun isa wurin kafin a fara daurin auren, an samu nasarar cafke mata 15 da maza 4.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Haruna Ibn Sina ya bayyana cewa an kama matasan ne bayan wani rahoto da wani mai kishin kasa ya kai wa hukumar game da auren jinsin.
Ya kara da cewa ‘yan luwadi biyun ‘ango da amarya’, Abba da Mujahid sun tsere bayan isowar jami’an Hisbah a wurin daurin auren.
Sai dai Ibn Sina ya bayyana cewa wacce ta shirya taron, Salma Usman mai shekaru 21 a duniya a halin yanzu tana hannunsu, hukumar za ta kara zage damtse wajen ganin an cafke Abba da Mujahid.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp