Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wasu motoci uku makil da kwalaben giya sama da 18,000 a karamar hukumar Gwarzo a jihar.
Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa an kama motocin dauke da giyar ne a ranar Litinin a hanyar Gwarzo a kan hanyarsu ta zuwa Kano.
- An gudanar da taron tunawa da marigayi Jiang Zemin
- Sin Ta Sauke Nauyin Dake Wuyanta Wajen Taimakawa Kasashen Da Suka Fi Rashin Ci Gaba
A cewarsa, dokar da ta kafa hukumar Hisbah ta Kano ta haramta siyar da kayan maye a kowane yanki na jihar.
“Hukumar na da manyan motoci sama da goma dauke da barasa a hannunta, kuma za ta bi tsarin da ya dace domin tabbatar da hukuncin kotu na lalata giyar, haka kuma hukumar ta kara kaimi wajen kamfe da shawarwari domin fadakar da jama’a illar hada barasa. cikin ayyukan fasiqanci.”
A yayin da yake yabawa sashen kula da abubuwan sa maye a bisa namijin kokarin da suke yi na dakile yaduwar barasa da sauran muggan kwayoyi a jihar, Sheikh Ibn Sina ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa shan giyar ya zama tarihi a jihar.