Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta haramtawa maza masu yin DJ (kaɗe-kaɗe) gudanar da kaɗe-kaɗe a yayin taron bukukuwan da mata suka mamaye, a duk fadin jihar.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da wakilan masu kaɗe-kaɗen a jihar.
- Hajjin 2024: Ranar 10 Ga Watan Yuni Za A Kammala Jigilar Maniyyata – NAHCON
- Jami’ar FUBK Ta Gudanar Da Bikin Ɗaukar Sabbin Ɗalibai 2, 217 A Kebbi
Sheikh Daurawa ya jaddada cewa, haramcin na da nufin hana cakuduwar maza da mata a lokutan bukukuwan al’umma, inda ya yi nuni da cewa, cakuduwa tsakanin maza da mata ya sabawa al’adar jihar da addinin Musulunci.
Ya jaddada cewa, kasancewar dokokin Musulunci jihar ke dogaro da shi, ya zama wajibi a kiyaye ka’idojin da ke hana ayyukan da ake ganin sun saba wa koyarwar Musulunci.
Sheikh Daurawa ya bayyana cewa, daga yanzu mata ne kawai za a bari su gudanar da taron mata.
Bugu da kari, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa, kafin yanke wannan hukunci, hukumar ta Hisbah ta hada hannu da masu cibiyoyin taro da manajojinsu a jihar domin wayar musu da kai kan dokokin da ke tafiyar da harkokinsu.
A nasa martanin, wakilin makaɗan, DJ Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da DJ Farawa, ya nuna godiya ga hukumar ta Hisbah bisa gayyata da jagoranci da aka yi musu.
Ya bayyana muhimmancin bin sabbin ka’idojin da hukumar ta bullo da su, musamman dangane da tsarkin lokutan sallah da kuma ware tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwan jama’a.
Abdullahi ya bukaci dukkan makaɗan da ke aiki a fadin jihar da su yi rajista da kungiyarsu domin tabbatar da bin ka’idojin hukumar ta Hisbah wanda yace, kungiyar ba za ta kare duk wani DJ da aka samu da laifi ba.