Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta shawarci ma’aurata da su san yanayin lafiyar abokan zamansu kafin su yi aure domin dakile yaduwar cutar karya garkuwar jiki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge, ya fitar a Kano.
- Akwai Alamun Ba Gudu Ba Ja Da Baya A Kan Batun Taiwan
- KECHEMA Ta Kaddamar Da Kwamitin Bayar Da Gudunmawar Kula Da Kiwon Lafiya A Kebbi
Fagge, ya bayyana cewa, mukaddashin Kwamandan hukumar, Hussain Ahmad, ne ya bayyana haka a lokacin da ya tarbi jagorancin kungiyar Achievers Improved Health Initiatives, AIHI, a shelkwatar hukumar da ke unguwar Sharada.
Ya nakalto mukaddashin kwamandan na tabbatar da cewa, hukumar za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga yunkurin da kungiyoyi masu zaman kansu ke yi na inganta lafiyar jama’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
“Hisbah za ta hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa domin kara wayar da kan jama’a kan illar cuta mai karya garkuwar jiki.
“Wannan ko shakka babu zai shawo kan yaduwar kwayar cutar da sauran cututtuka masu yaduwa a tsakanin jama’a,” in ji shi.
Tun da fari, kakakin AIHI, Ibrahim Hassan, ya ce sun kai ziyarar ne domin karfafa alakar aiki tsakanin kungiyoyin biyu domin amfanin jama’a.