Gwamnatin Honduras ta bude ofishin jakadancin ta a kasar Sin a yau Lahadi, watanni 2 bayan da ta kulla huldar jakadanci da kasar ta Sin.
Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan wajen kasar Qin Gang, da takwaransa na Honduras Eduardo Enrique Reina, sun halarci bikin kaddamar da ofishin.
Da yake tsokaci game da wannan ci gaba, Qin Gang ya ce saurin bunkasar alakar Sin da Honduras, ya shaida muhimmancin tsayawa kan kare manufar kasar Sin daya tak a duniya, manufar da akasarin sassan kasa da kasa ke marawa baya, wadda kuma ke wakiltar mahangar mafi rinjayen kasashen duniya.
Kaza lika, Qin ya ce ziyarar aiki da shugaban Honduras Xiomara Castro ke yi yanzu haka a kasar Sin na da ma’anar gaske, kasancewar ganawar shugabannin sassan biyu, za ta bayar da damar share fagen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen su.
Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Honduras, wajen zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban bisa martaba juna, da daidaito, da cimma moriyar juna, da samar da ci gaban bai daya, tare da mayar da alakar Sin da Honduras sabon salon kawance na hadin gwiwa, tsakanin kasashe dake da yanayi da tsare tsare mabanbanta.
A nasa bangare kuwa, Reina cewa ya yi Honduras za ta nacewa manufar kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma fatan alakar Sin da Honduras za ta ci gaba da karfafa, ta yadda za ta haifar da alherai masu yawa ga al’ummun su. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)