A yau Juma’a Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen jana’izar Sarkin Zuru, Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami (ritaya), wanda aka yi a garin Zuru, Jihar Kebbi.
A wajen jana’izar, Shettima ya jaddada gagarumar gudummawar da marigayi Sarkin ya bayar, waɗanda ya ce ba za a taɓa mantawa da su ba.
Ya ce, “Ana girmama sarakunan gargajiya a ƙasar mu saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.”
Shettima ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa wajen jana’izar kuma ya isar da gaisuwar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ga gwamnatin Jihar Kebbi da iyalan marigayin da kuma dukkan al’ummar jihar.
Ɗimbin sarakuna, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa da sauran mutane sun halarci taron jana’izar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp