Jami’an tsaro sun rufe hanyar shiga Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, biyo bayan yunkurin wasu ‘yan majalisar 22 na tsige Kakakin Majalisar, Abubakar Y Sulaiman da sauran shugabannin majalisar.
Idan za a iya tunawa ‘yan majalisar dokokin Jihar 22 sun kada kuri’ar rashin kwarin guiwar kan salon jagorancin majalisar, inda suka nemi shugabanninsu da su yi murabus ko su tsigesu.
- 2023: PDP Na Bukatar Hadi Kai Don Kayar Da APC – Makarfi
- Muna Yin Siyasa Ce Bisa Tsammanin Gaba Za Ta Yi Kyau –Hajiya Halimah
Ya zuwa yanzu dai majalisar na rufe a karkashin kulawar jami’an tsaron ‘yan sanda da wasu sauran jami’an tsaro.
Hotunan yadda Majalisar ke rufe da wakilinmu ya dauka yau Litinin.