Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa birnin Landan domin amsa goron gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta aike masa.

Daraktan kwamitin yakin neman zaben Atiku, Sanata Dino Melaye ne, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.

A cewar Melaye, a ziyarar aiki ta kwanaki biyu, Atiku zai gana da wasu jiga-jigan gwamnati.

Ya ce dan takarar na shugaban kasar tare da tawagarsa za su kuma gana da Archbishop na Canterbury, sannan za su halarci sauran shirye-shirye da aka tsara musu.
