Kamfani sadarwa na kasar Sin Huawei ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ma’aikatar kula da fasahar koyon sana’a da horaswa ko TVET a takaice ta kasar Kenya, don sa kaimi ga bunkasa kwarewar ma’aikatan kasar a fannin fasahar dijital.
Yarjejeniyar ta shekara uku, wacce aka daddale ta a lokacin bikin bayar da lambar yabo na gasar Huawei ICT na kudancin Afirka da aka kammala kwanan nan, na da nufin inganta kwarewar ma’aikata matasa na Kenya a fannin fasahar sadarwa ta zamani, a cewar Huawei a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kolin CELAC Karo Na 9
- Sin Ta Kara Buga Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigarwa Kasar Daga Amurka Zuwa 84%
Kazalika, babbar sakatariya a ma’aikatar ta TVET Esther Mworia ta ce “Wannan hadin gwiwa da kamfanin Huawei wani muhimmin mataki ne na baiwa matasan Kenya damar samun fasahar zamani da ake bukata don samun nasara a tattalin arzikin duniya.”
Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp