Babban kamfanin fasahar nan na kasar Sin Huawei, ya kaddamar da shirin horaswa game da tsaron yanar gizo ga jami’an sassan gwamnatin Zimbabwe. An kaddamar da kwas din ne a jiya Litinin a birnin Harare fadar mulkin kasa.
Kwas din na yini 4 ya samu halartar jami’an gwamnatin kasar 100, wadanda suka fito daga ma’aikatu da cibiyoyin gwamanti, kuma yana gudana karkashin hadin gwiwar kamfanin Huawei da ma’aikatar watsa labarai da fasahar sadarwa, da sashen gidan waya da aikewa da sakwanni na kasar.
- Xi Ya Gana Da Shugabannin Majalisun Dokokin Kasashen Duniya
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Sayar da Tireloli 300 Na Shinkafa A Farashi Mai Rahusa
An tsara horas da jami’ai mahalarta kwas din darussa masu nasaba da muhimman batutuwan tsaron yanar gizo dake shafar duniya, da tsaron yanar gizo a matakin kasa da kasa, da tsarin amfani da kafofi masu zaman kan su don kare yanar gizo, da na kare bayanai masu alaka.
Cikin jawabin da aka gabatar a madadin sa, babban daraktan kamfanin Huawei na kasar Zimbabwe Yang Shengwan, ya ce a nan gaba ma Huawei zai ci gaba da zuba jari a sashen raya harkokin dijital na kasar, zai kuma wanzar da aiki kafada da kafada da gwamnatin kasar wajen shawo kan kalubalolin tsaron yanar gizo.
A nasa bangaren kuwa, babban sakatare a ma’aikatar watsa labarai da fasahar sadarwa ta kasar Beaullar Chirume, ya yaba ne da irin gudummawar da kamfanin Huawei ke bayarwa a fannin raya ababen more rayuwar al’ummar Zimbabwe a bangaren na’urorin dijital. (Mai fassara: Saminu Alhassan)