“Zan fayyace maka a matsayina na uwar ‘ya’a hudu bakaken fata: maganar ita ce tsaron kai, kan abubuwan da za ka yi ka zauna a gida lafiya.”
Reberend Najuma Smith-Pollard ta san batun sosai, wadda ta aiwatar ga danta Daniel, wanda ya mutu a 2018 yana shekara 24, kuma yanzu tana da ‘ya’ya uku ‘yan shekara 12 da 17 da kuma 18, wani lokaci kuma da ‘yarta ‘yar shekara bakwai suna zaune a Kudancin Los Angeles.
Ba tattaunawa ba ce da ake yawan yi, batu ne da ake ambata lokaci daya, amma wanda ke ci gaba da wakana, da ke faruwa tsakanin iyalan bakaken fata a shekaru da dama.
“Tatattaunawa da ke ci gaba da gudana tsakanin iyaye da ‘ya’yansu game da yadda ya kamata su kare kansu a rayuwa ta yau da kullum,” in ji Smith-Pollard wadda take bayyana kwarewarta a matsayinta na malamar kirista kuma shugabar al’umma a wurin aikinta na Cibiyar Nazarin Harakokin Addini da Al’adu a Jami’ar Southern California (USC).
“A matsayina na uwar ‘ya’ya bakaken fata da ke zama a birni, ina magana da su game da ‘yan sanda da kuma masu laifi, domin akwai mutane makwabta wadanda ba su da mugunyar aniya.
“Ina koya masu yadda za su yi mu’amula da jami’an tsaro da kuma rayuwa gaba daya, a cewarta.
Wanda aka fi sani da “The Talk, shi ne da’awar yau da kullum na abin da masana ilimi ke kira launin fata da zamantakewar kabilanci, wanda fage ne na nazari a fannin ilimin zamantakewa da halayyar Dan‘adam.
Akwai dimbin rubuce-rubucen kimiyya game da maudu’in da shirye-shirye kamar ‘The Talk’: ‘Race in America’ da ake gabatarwa a kafar talabijin na PBS a Amurka.
Da yawa akwai wadanda suka yi magana da yan jaridu sannan kuma kwai wadanda suka ki amincewa, amma dai sun bayyana shirin “The Talk” a matsayin wani abu mai daci, wani nauyi da iyalan Amurkawa ‘yan asalin Afirka da Latino suke hakuri da shi.
“Yanzu da ake yawan samun rikicin wariyar launin fata, haka kuma dole mu fara fadar matasarmu cewa, kada ku taba yarda da fararen fata ‘yan shekara 18,” in ji Smith-Pollard.
Tana ba da misali da harin bindiga a ranar 14 ga Mayu da mutum 10 suka mutu a wani babban kanti a Bufallo, New York inda bakaken fata suka fi yawa.
‘Yansanda
“Ta tattauna tsakaninta da babban danta ne lokacin da ya kai shekara 13. Yana aji bakwai wasu suka kai masa hari a kan hanyarsa ta zuwa dakin karatu tare da abokin karatunsa.
“Dole na fada maka, a duk lokacin da kai da abokinka kuka fita, ka dinga kula da wanda kake tare da su.”
Wannan sakon game matakan tsaronsa ana maimaita masa a duk lokacin da zai fita shi kadai, amma abin ya sauya bayan ya samu lasisin tuki.
“Lokacin da ya fara tuki dole na fara magana da shi game da abin da ya dace ya yi da kuma abin da bai dace ba, idan har ka yi karo da ‘yan sanda,” in ji ta.
Tattaunawar ta fara ne kamar haka, kamar yadda take tunawa: “Mun zauna a Los Angeles, bangaren Kudanci.
Ba sai ka yi wani abu marar kyau ba kafin a kama ka. Za su iya cewa ka tsaya, su tuhume ka. Ya kamata ka san cewa kana da ‘yanci.” In ji ta.
Ta riga ta fada masa game da ‘yancinsa lokacin da ya cika shekara 15, saboda kamanninsa – shi dogo ne kuma kakkaura, ya buga wasan a kwallo Amurka tun yana shekara tara kuma yawanci mutane na daukarsa mai yawan shekaru.
“Kada ka bari wani ya fara bincikenka ba tare da yana da sammaci ba. Ba dole sai ka amsa tambayoyi ba, domin kai yaro ne. Za ka iya kiran mahaifiyarka, ka sa su kira ni nan-take.
“Kada ka damu idan har suna son tafiya da kai ofishin ‘yan sanda, kada ka yi fada kuma kada ka gudu. Mahaifinka da ni za mu yi kokarin fitar da kai daga ko wace irin fitina.”
“Ka fada masu sunanka kuma ka nuna masu katinka na shaida. Abubuwan da za ka ba su kenan, kuma ya fi dacewa su duba da kansu domin tabbatar da ba ka taba aikata laifi ba.