Hukumar ladaftarwa ta jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ko CCDI ta 20, ta fitar da rahoton aikin ta a yau Lahadi. Zaunannen mamba na hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS, kuma sakataren hukumar ta CCDI Li Xi ne ya gabatar da rahoton a ranar 8 ga watan Janairun da ta gabata, yayin zama na 3 na hukumar ta CCDI dake karkashin JKS.
Rahoton, wanda ya mayar da hankali ga ingiza matakan samar da ci gaba mai inganci a fannin sanya ido ga da’a da bin bahasi a sabuwar tafiya, da waiwayar aikin hukumar ta CCDI na shekarar 2023, da kuma fayyace ayyukan ta na shekarar 2024.
- Zaben Shugaban Kasar Amurka 2024: Afirka Ba Ta Shirya Fuskantar Wa’adi Na Biyu Na Shugabancin Trump Ba
- Gwamnatin Nijeriya Ta Nuna Halin Ko-in-kula A Lokacin Da Nake Tsare A Kurkukun Kasar Nijar -442
A cewar rahoton, ya wajaba hukumar ladaftarwa ta jam’iyyar kwaminis, da hukumomin sanya ido, su sauke nauyin da kundin tsarin mulkin jam’iyya, da kundin tsarin mulkin kasar Sin suka dora musu.
Kaza lika, CCDI na karfafa gwiwar hukumomin da su yayata tsare tsaren kyautata aiwatar da jagorancin kawunan su, da bunkasa aiki a fannin inganta zartas da manufofi, da tabbatar da da’a, da yaki da cin hanci.
Har ila yau, rahoton ya jaddada bukatar kawar da damar kyankyashe laifin cin hanci, da zurfafa tsarin gudanar da sauye-sauye, da karfafa ginshikan sanya ido, don tabbatar da da’a da sanya ido, da kyautata ci gaban tsarin gudanar da ayyuka na hukumomin bin bahasi da na sanya ido. (Mai fassara: Saminu Alhassan)